
Saurara a: Apple Podcast | Spotify | RSS
Adisu Abba wata mata ce mai shekaru 45 kuma uwa ga ‘ya’ya biyar. Ta fito daga Dikwa, Jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Tun kafin rikici ya tarwatsa rayuwarta, ta riga ta fara koyon aikin da zai zama ginshiƙin rawarta a cikin al’ummarta—ta koyi yadda ake taimaka wa mata wajen haihuwa.
An yi garkuwa da Adisu a hannun ‘yan ta’adda na tsawon shekaru uku,a wannan lokacin, ta taimaka wajen haihuwar jarirai biyar.
A wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI, mun bada labarinta da kuma abin da yake nufi yin aikin ungozoma yayin da take tsare a hannun ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Sabiqah Bello
Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Mu’azu Muhammad
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
