
Neman Yanci Da Kudin Fansa | RSS.com
Saurara a: Apple Podcast | Spotify | RSS
kuna gida kuna shirye-shiryen dare, bayan sallar isha’i. Rayuwarku na cike da kalu-bale, amma aƙalla kuna tare da iyalan ku. kwatsam, ba tare da gargadi ba, mahara dauke da makamai suka mamaye kauyen ku.
Suna baku umarni da ihu har baku iya gane me suke fada.
Tsoro ya ratsa jikinku. Kuna gudu cikin duhu, zuciyar ku tana bugawa tare da fatan tsira, kuna ta addu’a. Amma duhun dare be baku abin da kuke fata ba. Yan ta’addan sun gan ku, kuma Suka fito da ku!
Daga wannan lokacin, rayuwa kamar yadda kuka sani ta canza muku gaba ɗaya.
Wannan Jigon na #BirbishinRikici ya bada labarin Huaraira da kwanakin da tayi a tsare.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Sabiqah Bello
Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Al-amin Umar
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
