
Saurara a: Apple Podcast | Spotify | RSS
Christie Garba mace ce mai shekaru 38, uwa ga yara bakwai, wadda ke zaune a Billiri, Jihar Gombe, a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Ta kasance tana zaune a Jihar Yobe tare da iyalinta kafin rikicin Boko Haram ya addabi yankin. A wancan lokacin, hare-hare sun riga sun faru a wasu wurare kusa da su, amma ba su kai ga al’ummarsu kai tsaye ba.
Christie da iyalinta sun zauna kimanin watanni huɗu bayan hare-haren sun fara, amma yayin da rikicin ya ƙaru, sojoji suka gargadi mazauna yankin cewa lamarin ya yi tsanani sosai, ba zai yiwu su ci gaba da zama ba. Dokokin hana fita (curfew) da suka biyo baya sun sa rayuwar yau da kullum ta zama mai matuƙar wahala.
A wannan shirin na #BirbishinRikici mun ba da labarin yadda Christie da iyalinta suka koma Jihar Gombe da kuma yadda ta yi rayuwa ta hanyar fara sabon kasuwanci.
Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed
Marubuciya: Sabiqah Bello
Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello
Fassara: Rukayya Saeed
Edita: Aliyu Dahiru
Furodusa: Mu’azu Muhammad
Babban Furodusa: Anthony Asemota
Babban Mashiryi: Ahmad Salkida
