Site icon Occasional Digest

Yadda Uwa Ta Yi Jiran Labarin Garkuwa Da Yayanta

Saurara a: Apple Podcast | Spotify | RSS


Lokacin Ramadan ne, kuma Bintu Suleiman, wata uwa kuma ‘yar kasuwa mai shekaru 55 daga Ngoshe a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya, tana shirin buɗe baki tare da iyalanta.

Sai harbe-harbe ya fara, kuma cikin awa guda gidanta ya kama da wuta. Yayin da ‘yan ta’adda ke tattara mutane, ta samu damar tserewa tare da wasu daga cikin ‘ya’yanta da jikokinta zuwa cikin daji. Daga baya, ta gane cewa mutum huɗu daga cikinsu ba su tsere tare da ita ba. Suna wani wuri a cikin duwatsu.

A wannan shirin na #BIRBISHINRIKICI, mun ga yadda bayan harin, Bintu, wadda yanzu ta rasa matsuguninta, ke samun mafaka a wata makarantar firamare ta gwamnati a Pulka, yayin da har yanzu ba ta san halin da ‘ya’yanta da jikokinta suke ciki ba.


Mai Gabatarwa: Rukayya Saeed

Marubuciya: Sabiqah Bello

Muryoyin Shiri: Sabiqah Bello

Fassara: Rukayya Saeed

Edita: Aliyu Dahiru

Furodusa: Mu’azu Muhammad

Babban Furodusa: Anthony Asemota

Babban Mashiryi: Ahmad Salkida

Source link

Exit mobile version